Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Tace Zatayi Nazarin Shara'ar Kotun ECOWAS Kafin Ta Saki Kanar Sambo Dasuki


Nigeria Arms Scandal
Nigeria Arms Scandal

Sambo Dasuki dai yana tsare hannun jamiaan tsaro ne tun cikin watan Decembar bara duk ko da samun belin da hakan bai kai ga sakin sa ba domin sabbin tuhume-tuhume, baya tuhumar badakalar dala biliyan dari biyu da miliya dari daya kudin makamai da mallakar makami ba bisa ka’ida ba.

Lauyan Sambo Dasukin Joseph Daudu ya kalubalanci ‘yan jarida sailin da yake amsa tambayoyin cewa su gano inda aka adana Dasukin.

Daudu yace zasu ci gaba da dagewa domin ganin an saki Dasukin.

Wani mai marawa gwamnatin Buhari baya Yau Chiroman bakan Daura yace suna adawa da duk wani hukuncin sako Kanar Dasukin, sailin da suke tattaunawa da wakilin sashen Hausa Nasir Adamu El-Hikaya.Ga kuma abinda yake cewa.

‘’To wai a sako Sambo Dasuki, da sake Sambo Dasuki gara kaje ka saki dan fashin da ya samu Mutum da bindiga yayi masa fashi ya kashe shi domin shi mutum guda ya kashe shiko wannan jamaan kasa yayi wa illa.’’

Ga Nasir Adamu El-Hikaya da Karin bayani 3’06

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG