Yayin da ‘yan takarar neman zama gwamnan jihar Kebbi karkashin jam’iyyar PDP mai mulki ke ta fitowa, zargin shirin dauki dora ya fara mamaye harkokin siyasa a wannan jiha, inda wasu ke ganin Gwamna Usman Sa’idu Nasamu Dakingari na son dora wani dan yankin Kebbi ta tsakiya.
Haka zalika, baya ga zargin na yinkurin dauki dora, akwai kuma matsalar bangaranci da ta kunno kai. ‘Yan kudancin jihar, wadanda su ka ce an jima ana danne su a siyasance, sun ce wannan karon ba fa za su yadda ba.
Wani dan dakarar gwamnan jihar daga kudanci, Janar Muhammadu Magoro (murabus), ya ce sai da ‘yan kudancin jihar su ka yi tawaga zuwa wurin gwamnan su ka gabatar masa da kokensu na bukatar kudanci ya fito da gwamnan jihar wannan karon, kuma ya nuna goyon bayansa. Saboda haka, in ji shi, da ban mamaki kuma ace wai gwamnan ya fito da wani daga wani bangare daban.
Shugaban kungiyar fafatukar neman ganin yankin na kudu ya fito da gwamna mai suna Dantanin Zuru, ya ce lallai akwai batun karba-karba a jam’iyyar PDP, don haka muddun aka ki barin yankin ya fito da dan takakar gwamna to za su bar jam’iyyar PDP.
Your browser doesn’t support HTML5