Shi dai Donald Trump attajiri ne na gaske wanda ya gaji tarin dukiya daga mahaifinsa, musamman dukiyar arzikin gine-gine.
Donald Tumpp ya tara dukiya mai tarin yawa daga gine ginen benaye na ofisoshi da na otel otel da gidajen caca da filayen wasan kwallon gwalf da ma wasu manyan gine gine a fadin duniya.
Shi ne shugaban rukunin kamfanonin Trump dake gina gidajen haya da kamfanonin masana'antu hade da wasu harkokin kasuwancinsa.
An haifi Donald Trump ne a gudumar Queens dake birnin New York kuma ya girma ne a anguwar masu hannu da shuni da aka fi sani da suna Jamaica Estate.
Donald J. Trump na cikin 'ya'ya biyar da mahaifinsa Fred Trump ya haifa. Mahaifin nasa sanannen attajiri ne da shi ma yayi suna wajen gine ginen gidaje. Haka kuma Fred mutum ne mai son mulki kuma bisa ga duk alamu dansa Donald Trump ya gajeshi.
A shekarar 1968 ne Donald Trump ya kammala karatun jami'a inda ya karanta fannin kasuwanci a kwalajin Wharton dake cikin Jami'ar Pennsylvania.
Da yake mahaifinsa sana'ar gine gine ya keyi a birnin New York shi ma sai ya maida hankali a kan sana'ar amma a anguwar Manhattan.
A shekarar 1970 ne hukumomi suka zargi ma'aikatansa da nuna banbancin kabilanci wurin ba da gidajen haya. Ba sa bada gidaje ga marasa galihu. To saidai Donald Trump ya sasanta batun a kotu.
Donald Trump yayi wani babban yunkuri yayinda ya sayi ginin wani kasaitaccen otel dake kusa da wata babbar tashar jiragen kasa ta Grand Central.
Amma an fi saninsa da ginisa na Trump Towers wanda aka kiyasata kudinsa ya kai dala miliyan dari biyu mai cike da kayan alatu da kawa, makeken bene mai hawa hamsin da takwas wanda ya kunshi gidajen zama da shagunan kyece reni.
Donald Trump ya shahara wurin gina gidajen caca musamman a birnin Atlantic City dake jihar New Jersey inda ya mallaki manyan gidajen caca fiye da ukku. Daya daga cikinsu da ake kira Tajmahal an kashe kudi fiye da dala miliyan dubu daya wajen ginashi.
To saidai gidajen cacan sun wargaje domin sun kasa mayar da riba.
A lokacin da kasuwancin gine gine ya fuskanci rushewa a shekarar 1990 arzikinsa ya ragu daga dala biliyan daya zuwa dari biyar kawai. A karshe ma sai da ya ranci kudi kuma ya samo sabbin masu saka jari.
Saidai wani abun da Trump ya kasa kaucewa shi ne yawan auratayya da kuma yawan sakin matan da yake aura lamarin da ya sa rigimarsa da mata ta dinga fitowa a kafofin yada labarai.
Matarsa ta farko da ya saka wadda suka samu 'ya'ya ukku tsakaninsu ita ce Ivanka. Bayan mutuwar aurensu ya auri Mala Mapos wadda ya saketa bayan wani dan lokaci.
A shekarar 2005 Donald Trump ya auri matarsa ta yanzu Melania mai son kayan ado kuma tana nuni kayan adon. Yar kasar Slovenia ce.
Wani wasan kwaikwayo na talibijan mai suna The Apprentice ya maida Trump tamkar wani gwarzo. Shirin ya samar masa zunzurutun kudi da suka haye dala miliyan dari biyu.
A shekarar 1980 ne Donald Trump ya soma nuna sha'awar shiga siyasa lokacin da ya shiga jam'iyyar Reform Party daga bisani kuma ya koma jam'iyyar Democrat.
Ya tsaya takara a matsayin dan indipenda. A shekarar 2012 ne kuma ya canza sheka zuwa jam'iyyar Republican. Tun daga lokacin ne ya fara anfani da taken "Zamu Sake Farfado da Martabar Amurka".
A matasyinsa na dan takara Donald Trump yayi kamarin suna wajen fadan kalaman cin mutuncin jinsunan mutane daban daban da suka hada da bakin hauren 'yan kasar Mexico wadanda ya zarga da shiga Amurka da miyagun kwayoyi.
Ya kara da cewa zai gina katafariyar katanga akan iyakar Amurka da Mexico kuma yace kasar ta Mexico ce zata biya kudin ginin. Trump ya cigaba da maganganun tsokana da sukan lamirin mutane iri iri tare da cewa zai haramtawa Musulmi shigowa Amurka.
Ga fasarar Baba Yakubu Makeri da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5