Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Rantsar da Donald Trump A Matsayin Shugaban Amurka Yau


Donald Trump da iyalansa
Donald Trump da iyalansa

A cikin jadawalin bikin rantsar da Dolad Trump da mataimakinsa da za'a yi yau an shirya a soma bikin da karfe tara da rabi na safe agongon Amurka kana a kammala da karfe biyu da minti arba'in da biyar

Za'a bude bikin da misalin karfe tara da rabi na safe da wakoki da mawakan Mijami'ar Katolika dake nan Washinton DC zasu rera.

Bayan sun rera waka ta minti goma sha ukku mawakan da makidan sojojin kuntunbala zasu rera tasu wakar irin ta sojoji.

Da karfe goma da minti ishirin da biyu tsoffin mataimakan shugabannin kasar zasu shigo su zauna. 'Yan Majalisar Wakilai zasu bi bayansu su ma su zauna sai kuma gwamnonin jihohi.

Sanatoci zasu zauna da karfe goma da minti talatin da biyu kuma cikin mintuna hudu wadanda aka gabatar da sunayensu ga Majalisar Dattawa domin basu mukaman ministoci zasu biyo bayan Sanatocin.

Alkalin alkalan Amurka zai shigo da karfe goma da minti arba'in da hudu. Da zara ya zauna sai tsoffin shugabannin kasa su shigo su zauna.

Kusan lokaci guda 'ya'yan mataimakin shugaban kasa mai jiran gado da 'yanyan shugaban kasa mai jiran gado zasu shigo su zauna.

Michelle Obama uwargidan shugaban kasa mai barin gado da Dr. Jill Biden matar mataimakin shugaban kasa mai barin gado zasu shigo su zauna.

Minti ukku bayan da su Michelle suka zauna matan Trump da Pence mataimakinsa zasu shigo su zauna.

Da misalin karfe goma sha daya da minti tara mataimakin shugaban kasa mai jiran gado, Mike Pence zai kama tashi kujerar zama. Bayan minti biyar shugaban kasa mai jiran gado Donald Trump zai shigo ya zauna.

Za'a fara rantsar da mataimakin shugaban kasa da karfe goma sha daya da minti talatin da biyar. Bayan mintin goma cur za'a gabatar da alkalin alkalan kasar wato John Roberts.

Alkalin alkalai John Roberts zai rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban kasa da karfe goma sha daya da minti arba'in da bakwai. Bayan 'yar waka ta minti daya sai a yi harbin bindiga sau ishirin da daya da gaisuwar ban girma ga sabon shugaban kasa. Bayan nan sai a gabatar wa Amurkawa da duniya sabon shugaban kasa.

Sabon shugaban kasa Donald Trump zai yi jawabinsa na farko a daidai karfe goma sha daya da minti hamsin da daya na mintuna ishirin da daya kawai.

Donald Trump na gama jawabinsa za'a gudanar da addu'o'i sannan da karfe goma sha biyu da minti hamsin da hudu a shiga dakin rabtaba hannu ga wasu takardu na musamman.

Akwai lokacin bada kyaututtuka da za'a fara da misalin karfe biyu.

Da misalin karfe biyu da minti arba'in da biyar Shugaban kasa Trump da matarsa da Mataimakin shugaban kasa Pence da matarsa zasu bar wurin bikin tare da sojoji masu pareti.

XS
SM
MD
LG