Hukumar Kwallon kafar Najeriya NFF ta sanar da nada Bruno Labbadia a matsayin sabon mai horar da ‘yan wasan Super Eagles.
Hukumar ta NFF ta sanar cewa ta cimma matsaya da Labbadia dan asalin kasar Jamus, wanda shi ne koci na 37 da zai horar da ‘yan wasan na Najeriya.
“Hukumar NFF ta amince da shawarar da kwamitin tsare-tsare ya bayar na nada Mr. Bruno Labbadia a matsayin kocin Super Eagles. Nadin zai fara aikin nan take.” In ji Sakatare-Janar na NFF, Dr. Mohammed Sanusi.
An haifi Labbadia a Darmstadt, Jamus a ranar 8 ga watan Fabrairun 1966.
Labbadia ya samu nasarori da dama a rayuwarsa ta harkar kwallon kafa inda ya taka leda kungiyoyin kwallon kafa irinsu Darmstadt da ke mahaifarsa, Hamburger SV, FC Kaiserslautern, Bayern Munich, FC Cologne, Werder Bremen da Armenia.
Sauran kungiyoyin da ya yi aiki da su sun hada da Bielefeld DA Karlsrusher SC a gasar Bundesliga.
Ya kuma taba bugawa Bayern Munich wasa a shekarar 1994.
Labbadia ya kuma horar da kungiyoyin Hertha Berlin da VfB Stuttgart, VfL Wolfsburg, Hamburger SV, Bayer Leverkusen yana kuma da lasisi horarwa na UEFA.
Babban kalubalen da ke gaban Labbadia shi ne tabbatar da zuwan Najeriya gasar cin kofin nahiyar Afirka na AFCON a 2025 inda Super Eagles za ta kara a wasan neman gurbi da Benin Republic a ranar 7 ga watan Satumba a birnin Uyo.
Sai kuma wasan da Najeriya za ta kara da Rwanda a ranar 10 ga watan Satumba a birnin Kigali.
Akwai sauran wasanni hudu da za su biyo baya na neman gurbin shiga gasar a watannin Oktoba da Nuwamba.