Rasuwar Tandja Mamadou Da Takaitaccen Tarihinsa

Tandja Mamadou

Daukacin Janhuriyar Nijar, kama daga mahukunta da magabata zuwa talakawan kasar da ma na kasashen ketare, na cigaba da alhinin rasuwar tsohon Shugaban Janhuriyar Nijar, Tandja Mamadou.

Kamar yadda ba a rasa ji ba, Allah ya yiwa tsohon shugaban kasar Nijer, Tandja Mamadou, rasuwa a jiya Talata 24 ga watan Nuwamba a babban asibitin Yamai bayan fama da rashin lafiya. Shugaba Issouhou Mahamadou ya ayyana zaman makoki na tsawon kwanaki 3 a fadin kasar don nuna juyayin wannan babban rashi.

A sanarwar da aka bayar a kafar talabijin mallakar gwamnatin Nijer ne aka bayyana wa jama’a rasuwar tsohon shugaban kasa Tandja Mamadou, wanda Allah ya yiwa cikawa da yammacin jiya Talata, bayan jinyar da ya yi a babban asibitin Yamai .Salissou Mahaman Habi shi ne Ministan Yada Labaran jamhuriyar Nijer.

Mamadou Tandja

Hafsan soja a zamanin gwamnatin Janar Seini Kountche, Tandja Mamadou ya tube kakinsa a wajejen 1991, inda ya tsunduma cikin harkokin siyasa a karkashin tutar jam’iyyar MNSD, abin da ya bashi damar lashe zaben Shugaban kasa sau 2 wato a 1999 da shekarar 2004 kafin sojoji su kifar da gwamnatinsa a ranar 18 ga watan Fabrairun 2010, watanni kadan bayan zarcewa akan karagar mulki ba bisa ka’ida ba. Jami’in fafutuka, Nouhou Mahamadou Arzika da ke daya daga cikin makusantan marigayi Tandja Mamadou ya bayyana kaduwarsa da wannan babban rashi a hira da Muryar Amurka.

An haifi Tandja Mamadou a 1938 a garin Maine Soroa dake jihar Diffa. kafin dare kujerar shugabancin Nijer, hafsan sojan ya yi gwamna a jihar Tahoua, sannan ya yi Minista a zamanin mulkin soja. Tandja Mamadou na da farin jini sosai a wajen al’umma, saboda yadda ya ke fifita ayyukan bunkasa karkara da nufin faranta wa talaka rai.

Tsohon Shugaban Janhuriyar Nijar, Tandja Mamadou, ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya da jikoki da dama.

Ga Souley Barma da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Rasuwar Tandja Mmamadou