Takaddamar Jami'an Tsaron Najeriya Kan Sace 'Yan matan Dapchi

Niger: Addu'ar a sako 'yan matan Chibok da Dapchi

Masana a Najeriya, na ci gaba da tsokaci, kan cece-ku-cen da ke faruwa tsakanin jami’an tsaro game da yadda aka sace ‘yan matan Dapchi a jihar Yobe.

Gwamnan jihar Yobe Alhaji Ibrahim Geidam, ya zargi sojoji da janye wa daga garin Dapchi, al’amarin da ya bai wa mayakan Boko Haram damar zuwa su sace ‘yan matan sakandaren gwamnatin da ke jihar.

Sai dai kuma cikin sanarwar da ta fitar, rundunar Operation Lafiya Dole, da ke yaki da Boko Haram a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, ta ce babu gaskiya a kalaman na gwamna Geidam, inda ta ce ba ta janye sojojinta daga garin Dapchi ba.

Abin da ya faru shi ne sojojin sun kai dauki ne garin Kanamma da ke kan iyakar Najeriya da Nijar bayan wani hari da aka kai a yankin.

Sojojin na cewa kafin su fita su bar garin Dapchi sun mika tsaron garin ne a hannun rundunar ‘yan sanda, batun da rundunar ‘yan sandan jihar ta Yobe su ma suka musanta.

Cikin wata sanarwa da kwamishinan ‘yan sandan jihar Yobe, Alhaji Abdulmakil Sumonu, ya aikawa manema labarai, ya ce sanarwar da sojoji suka fitar ta cewa sun mika musu garin Dapchi ba gaskiya ba ne.

Da yake fashin baki kan wannan cece-ku-cen da ke faruwa tsakanin jami’an tsaron, Farfesa Mohammed Tukur Baba, ya ce, wannan lamari na da daure kai, ganin yadda ‘yan Boko Haram suka sake sace dalibai kamar yadda suka yi a garin Chibok.

Farfesa Mohammed na ganin babu hadin kai tsakanin jami’an tsaron kasa.

Alhaji Adamu Mohammed daya daga cikin iyayen da aka sace musu ‘ya'ya, na ganin wannan cacar bakin ba ta da wani amfani gare su, yana mai fatan ganin yadda za su mayar da hankali wajen ganin an samo musu ‘ya‘yansu.

Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

Takaddamar Jami'an Tsaron Najeriya Kan Sace 'Yan matan Dapchi- 2'23"