Mataimakin Gwamnan na mai da martani ne game da sanarwar da gwamnatin jihar ta bayar cewa shi Mataimakin Gwamnan jihar da kansa ne ya bukaci a masa uzuri daga halartar taron Majalisar Jihar. Yace, “A hakikanin gaskiya, shi Gwamnan Naija ne y ace ba zai yiwu a zauna a yayin da su ke gudanar abubuwa na Majalisar jiha ba, saboda ni ba dan jam’iyyar PDP ba ne. Alal hakika, ya iya nuna cewa ma, hasali, an kawo mashi “recording” na inda na ke cewa shi barawo ne da sauransu; kuma na tashi na ce ba haka ba ne.”
Da wakilnmu na Naija, wanda ya aiko da rahoton Mustafa Nasiru Batsari, ya tambaye shi matsayin da ya dauki kansa, sai y ace har yanzu shi ne Mataimakin Gwamnan jihar Naija kuma har yanzu shi mamba ne a Majalisar Jihar.
Da Mustafa ya tambayi wani lauya mai suna Abdulmalik Sarkin Daji matsayin wannan takaddamar a kundun tsarin mulkin Nijeriya, sai ya ce lallai Gwamna na da dinbin iko, to amma bai da ikon hana Mataimakinsa zama a Majalkisar Jihar saboda shi ma Mataimakin mamba ne. Y ace don kawai Mataimakinsa ya canza sheka, Gwamna bai da hurumin hana shi zama a Majalisar jiha.
Your browser doesn’t support HTML5