Takaddamar da ta kaure tsakanin Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara da wanda ya gada Bello Matawalle, wanda shi ne Ministan Tsaro na ci gaba da daukar sabon salo.
Gwamna Lawal da Minista Matawalle, na zargin juna da hannu a ayyukan barayin daji ke yi a jihar ta Zamfara wacce ke arewa maso yamacin Najeriya.
Jihar na daga cikin jihohin da ke fama da matsalar tsaro a yankin arewacin Najeriya.
A makon da ya gabata, Lawal ya yi kira ga Matawalle da ya yi murabus daga mukaminsa na minista don a bincike shi kan zargin alaka da ‘yan bindigar.
A cewar gwamnan, suna da bayanai da ke nuna cewa Matawalle na da alaka da barayin daji yana mai cewa babu adalci a ce mutumin da ake yi wa irin wannan zargi a ce shi ne ministan tsaron kasa.
"Kamata ya nuna dattaku, ya yi murabus don ya wanke kansa." Gwamna Dauda ya ce.
Sai dai a ranar Talata, yayin wata hira da Channels TV, Matawalle ya nesanta kansa da zargin alaka da ‘yan bindigar.
Matawalle ya kalubalanci masu zarginsa nasa da su rantse da Al Qur’ani Mai Girma cewa ba su da hannu a sha’anin ‘yan bindiga a jihar.
“Ina kalubalantar wadanda suke zargi na da su rantse da Al Qur’ani kamar yadda na yi cewa ba su da alaqa da ‘yan bidniga.
Ya kara da cewa idan kuma suka ki, “suna da hannu kenan.” In ji Matawalle.