Takaddamar Amurka Da Mexico Kan Kwararar Bakin Haure

Har yanzu akwai rashin tabbas da kuma damuwa a duka bangarorin biyu na iyaka bayan da shugaba, Donald Trump, a yau Litinin ya yi ikirarin cewa Amurka ta rattaba hannu, a abin da ya kira “wata muhimmiyar yarjejeniya da ta shafi shigar bakin haure kasar da kuma tsaro tare Mexico.”

Trump ya ki ya bayyana karin bayani akan abubuwan da ke ciki, kuma jami’an Mexicon sun musunta wani bangare na yarjejeniya kan kwararar bakin haure.

Ga dukkan alamu, misali ne na shirye shiryen yarjejeniyar masu neman mafaka a yankin baki daya idan aka tabbatar da daukan matakan da suka amince da su a satin da ya gabata tsakanin Washignton da Mexico City don hana karuwa bakin haure daga Taskiyar Nahiyar Amurka zuwa Amurka.

“Mun amince da matakan da muke dauka da muka gabatar da kuma muke fatan samun nasara, “Ministan Harkokin Wajan Mexico, Marcelo Ebrard, ya fadawa yan jaridu yau litinin. Amma idan basu amince ba, zamu ci gaba da shiga irin wannan tatattaunawa.

A lokacin da ake tambayar sa a Mexico City kan wani bangare na doka da Mexico ta amince na ci gaba da kara siyan kayayyakin gona daga Amurka, yayin da Trump ya ke ba da shawara a wani sakon Twitter da ya wallafa, Ya ce Ebrard kawai ya ce, “matsalar bakin haure daban take da harkar cinikayya.