Takaddama Ta Kunno Kai A Majalisar Dattawa Akan Batun Cire Wani Sashe Na Dokar Zabe

Majalisar Dattawan Najeriya (Facebook/Majalisar Dattawa)

Takkadama ce ta kunno kai a Majalisar Dattawa kan batun daukaka kara da majalisar dokoki kasar ta ce za ta yi, a game da hukuncin cire sashe na 84 karamin sashe na 12 daga sabuwar dokar zabe ta shekara 2022.

ABUJA, NIGERIA - Hakan ya faru ne domin daya cikin sanatoci ya ce ba a tuntube shi ba, saboda haka a cire sunan sa daga jerin sunayen masu goyon bayan daukan mataki akan dokar, daga bangaren Atoni Janar na kasa kuma, mai magana da yawunsa ya ce aikin gama ya gama.

Hukuncin da kotun tarrayya ta Umahia ta yanke cewa a soke sashi na 84 karamin sashi na 12 daga cikin sabuwar dokar zabe ta shekarar 2022 yana tada jijiyoyin wuya har ya kai ga raba kawunan ‘yan majalisar dattawa domin daya cikin su, Sanata Sani Musa daga Jihar Neja ya ce ba a tuntube shi ba kafin aka sa sunan sa a jerin wadanda suke goyon bayan matakin da Majalisar ta dauka cewa za ta daukaka kara akan hukuncin.

Ku Duba Wannan Ma Majalisar Dattawa Ta Ki Amincewa Da Bukatar Shugaba Buhari Ta Neman Gyara Sabuwar Dokar Zabe

Amma mataimakin mai tsawatarwa kuma Sanata mai wakiltan Jihar Neja ta Arewa Aliyu Sabi Abdullahi ya ce duk da takaddamar da ta kunno kai, Majalisar ba ta yarda a yi mata katsalandan a aikin ta ba.

To sai dai mai magana da yawun Ministan Shari'a kuma Atoni Janar na kasa Umar Jibril Gwandu ya ce, babu abinda zai hana a cire wannan sashi na 84 karamin sashi na 12 daga cikin dokar zabe, domin ta yi wa kundin tsarin mulkin kasa karan tsaye.

Ita ma Majalisar wakilai tare da Majalisar dattawa za su daukaka karar, domin ta haka ne kawai za a yi wa tukka hanci nan gaba.

Saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda:

Your browser doesn’t support HTML5

Takaddama Ta Kunno Kai A Majalisar Dattawa Akan Batun Cire Wani Sashe Game Da Dokar Zabe