JIGAWA, NIGERIA - Takaddamar ta nemi kaurewa ne tsakanin gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar cikin su kuwa har da tsohon gwamnan jihar Badaru Abubakar, dangane da zaben shugaban majalisar dokokin jihar.
Bayanai da muka tattara daga kafofin masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC a jihar ta Jigawa sun nuna mutane uku ne ke takarar shugabancin majalisar dokokin jihar, cikin su kuwa har da tsohon shugaban da ya kammala wa’adin sa a watan jiya, wato Hon. Idris Garba Kareka.
Rahotanni sun ce tsohon gwamna Badaru Abubakar da wasu kusoshi na Jam’iyyar na goyon bayan tsohon shugaban ya yi kome, yayin da sabon gwamna Malam Umar Namdi ke son a sami sabon hannu.
Amma, sakataren labarai na Gwamnan jihar Malam Hamisu Mohammed Gumel ya ce “ko kadan gwamma Malam Umar Namadi ba shi da hannu akan wa ye zai zama shugaban majalisar dokoki, saboda hurumi ne na majalisar kawai kuma majalisa bangare ne mai cin gashin kan ta a bisa tanadin kudin tsarin mulkin kasa”.
Ko da yake, an yi tarukan masu ruwa da tsaki iri-iri domin samun dai-daito, amma an gagara cimma matsaya, al’amarin da ya sanya tilas zaben sabon shugaba da rantsar da sabbin ’yan majalisar faskara a Talatar nan.
Ga alama wannan takaddamar ta kara jefa ‘yan majalisar dokokin ta Jigawa cikin yanayi na rudani.
Hon. Mohammed Kabiru Ibrahim sabon ‘dan majalisar dokokin mai wakiltar mazabar Birnin Kudu a karkashin inuwar Jam’iyyar PDP ya ce “Ka san ni sabon ‘dan majalisa ne wanda nake jira a rantsar da ni, gaskiya ba zan iya cewa, ga abin da yake faruwa ba, da ance za’a rantsar da mu 13 ga wata, yanzu kuma ance 14 ga wata, amma dai ko ma menene ba zai rasa nasaba da batun wa ye zai zama shugaban majalisa ba”.
Rashin kaddamar da majalisar ne ya sanya wasu matasa suka gudanar da zanga-zanga zuwa gidan gwamnati a Dutse da kuma harabar majalisar dokokin.
Sai dai bayanai na nuni da cewa, nan gaba a yau ne ake sa ran za’a kaddamar da majalisar bayan da gwamnan jihar ya aika wasikar kaddamarwar, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya shata.
Saurari cikakken rahoto daga Mahmud Ibrahim Kwari:
Your browser doesn’t support HTML5