Rahoton mutuwar dalibi Marwan Nuhu Sambo na makarantar Al-Azhar Academy Zariya dai ya fara bayyana ne a ranar Asabar da ta gabata duk kuwa da cewa dukan dalibin da mutuwar shi duk a Juma'a a ka yi.
Bayan bayyanar mutuwar dalibin ne kuma takaddama ta barke kan cewa iyayen dalibin ne suka hukunta shi saboda ba ya zuwa Makaranta abun da iyayen dalibin suka karyata suna masu bayyana ganganci kan kisar dan nasu sanadiyyar duka.
Shugaban kungiyar iyayen yara da malamai na Makarantar ta Al-Azhar Academy da ke Zaria, Malam Mujahideen Aminuddeen ya yi bayanin abun da ya faru, inda ya dage kan cewa rahoton da su ka samu iyayen dalibin suka kai shi makarantar don ladabtar da shi saboda rashin zuwa makaranta.
Sai dai kuma aminin mahaifin dalibin da aka kashe, Hon. Lawal Balarabe ya ce mahaifin yaron bai ce a hukunta yaron ba kuma hukuncin dukan na cike da wauta.
Inda ya ce dukan da aka yi ya sabawa dokar hukunta dalibai a makaranta.
Malam Ja'afar Balarabe, babban abokin mahaifin dalibi Marwan Nuhu Sambo ne kuma shi ya kai marigayin makarantar da bayan tafiyar shi aka sanar da shi labarin mutuwar marigayin.
Hukumar Makarantar ta Al-Azhar Academy Zariya dai ta tabbatar da cewa abun da ya faru dai kaddara ce kuma ta karbi kuskuren da malaman da su ka yi dukan su ka yi, inji magatakaddan Makarantar Malam Bashir Danraka.
Yanzu haka dai Gwamnatin jahar Kaduna ta sanar da rufe Makarantar ta Al-Azhar Academy Zariya yayin da rundunar 'yan-sandan jahar Kaduna ta tabbatar da kama wasu jami'an Makarantar don binciken wannan lamari inji Mai-magana da yawun rundunar 'yan-sandan jahar Kaduna, ASP Mansur Hassan.
Yanzu dai sanar da kulle wannan makaranta ana tsakiyar karatu ya jefa iyayen yara cikin damuwa har wasu sun fara tambayar ina makomar karatun 'ya'yansu tun da sauran makarantu suna ta karatu.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5