Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Ki Amincewa Da Matsayar Abdulmalik Da Ya Ce Ba Shi Ya Kashe Hanifa Ba


Abdulmalik Muhammad Tanko malamin makarantar da ake tukuma da garkuwa da kuma kashe dalibarsa Hanifa Abdullah
Abdulmalik Muhammad Tanko malamin makarantar da ake tukuma da garkuwa da kuma kashe dalibarsa Hanifa Abdullah

A ci gaba da sauraron shari'ar Abdulmalik Tanko da wasu mutane biyu wanda ake tuhuma da laifin kashe dalibar makaranta 'yar shekaru hudu wato, Hanifa, a yau alkalin babbar kotun Kano Mai Sharia Usman Na'abba ya yanke hukunci.

Wannan na zuwa ne biyo bayan bukatar lauyoyin shi Abdulmalik Tanko ta musanta laifin da ake zarginsa da aikatawa.

Tun gabanin gurfanar da shi a gaban kuliya, Abdulmalik Tanko ya shaidawa ‘yan sandan dake bincikar lamarin cewa, shi ne ya sace kuma ya yi garkuwa da yarinya Hanifa, kana daga bisani ya kashe ta tare da sassara sassan jikinta.

Hanifa dai daya ce daga cikin daliban makarantar shi Abdulmalik dake Unguwar Dakata a nan birnin Kano.

Sai dai bayan fara gabatar da shaidu a gaban babbar kotun Kano karkashin jagorancin Justice Usman Na’abba, a yayin zaman kotun na makon jiya sai kawai Abdulmalik Tanko ya musanta wancan ikirari na sa na fari, yana mai cewa, tilasta masa aka yi ya amsa laifin.

An Gurfanar da Masu Kisan Hanifa a Kotu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Nan take dai lauyoyinsa suka gabatar da bukata ta musamman, suna masu rokon kotu ta yi nazari akan wannan hanzari na a Abdulmalik Tanko tare da amincewa da abin da ya ambata.

Daga nan ne alkalin kotun ya dage zaman zuwa yau Laraba, ranar da zai bayyana matsayin kotu game da bukatar Abdulmalik da lauyoyinsa.

Hakan kuwa, akayi, inda jim kadan da fara zaman kotun, mai shari’a ya ce bayan nazari na tsanaki, kotu ta gamsu bisa hujjoji cewa, Albdulmalik Tanko ya amsa laifin hallaka dalibar makarantarsa Hanifa bisa radin kansa kuma babu yanayi na tilastawa game da hakan.

A don haka kotun ta ci gaba da karbar shedun lauyoyin gwamnati akan shari’a.

Babu Wanda Ya Illata Jikin Hanifa-Abdulmalik
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Barriter M.A Lawan dake zaman babban Atoni na Kano kuma kwamishinan shari’a na jihar shi ne ke jagorantar lauyoyin na gwamnati, ya kuma ce kotu ta yi hukunci inda ta tabbatar da bayanan wanda ake tuhuma na farko da na uku bisa ka’ida kuma ba tare da wani takurawa ko muzgunawa ba.

Shi ma dai Barr. M.L Usman dake kare Abdulmalik Tanko a wannan shari’a na cewa, kotun ta ba da na ta ra’ayin dangane da shara’ar, ta kuma zartar da hukunci akai kuma sai bayan kotu sun gama kawo shaidunsu, su kuma za su kawo nasu kariyar.

A makon jiya ne dai, kotun majistire ta Kano ta wanke Malama Fatima, wato mai dakin shi Abdulmalik Tanko daga wannan zargin na kisan gilla ga Hanifa Abubakar.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG