Wannan umurnin na ministan shari'ar Najeriya ya haddasa cecekuce tsakanin manyan layoyin kasar.
Yakubu Saleh Bawa wani babban lauya yace abun dake faruwa a jihar Rivers wani abu sabo ne. Tunda babu babban alkali, shugaban kotunan gargajiya na jihar ya kamata ya rantsar da gwamnan amma ba wani alkali daga wata jiha ba. Yace duk alkalan Najeriya suna karkashin alkalin alkalan kasar ne. Saboda haka ministan shari'a bashi da hurumin ya ce wani alkali daga wata jiha ya rantsar da sabon gwamnan Rivers.
Shi ma Barrister Aliyu Umar wani babban lauya yace ba daidai ba ne Atoni Janar na Najeriya ya bada umurnin da ya bayar domin bashi da ikon ya dauki aikin babban alkalin Rivers ya baiwa babban alkalin Bayelsa. Ko an yi hakan za'a kalubaleshi.
A daya bangaren kuma Barrister Yakubu Saleh Bawa yace kodayake jihar bata da babban alkali shugaban kotun gargajiya ko Grand Kahdi ko alkalin daukaka kara dake jihar ka iya rantsar da sabon gwamnan jihar.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina.
Your browser doesn’t support HTML5