Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jonathan Ta Kammala Shirin Mika Mulki


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan mai barin gado
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan mai barin gado

Saboda shakku da cecekuce da wasu ke yi akan ko dagaske za'a mika mulki ranar 29 ga wannan watan, gwamnatin Jonathan tace ta kamma shirin barin gado da mika mulki.

Majalisar zartaswa tayi taro na kusa da na karshe inda ta tsara hanyoyin da za'a bi saboda tabbatar da mika mulki cikin ruwan sanyi ba tare da wata matsala ba.

Taron ya zo a daidai da lokacin da ake rade-radin cewa akwai wasu matsaloli da ake fuskanta game da mika mulki, musamman tsakanin kwamitin dake shirin mika mulki da kuma kwamitin dake shirin karbar mulki. Ministar yada labarai ta gwamnatin Jonathan ta ce tuni an dauki duk matakan da suka kamata domin a tabbatar ba'a fuskanci wata matsala ba.

Sanata Patricia Akwashiki ministar watsa labarai tace ranar 28 ga wannan watan shugaban kasa mai barin gado Goodluck Jonathan zai nunawa sabon shugaban fadar shugaban kasa tare da mataimakinsa. Ran nan din Jonathan zai mikawa Janar Buhari sabon shugaba takardar bayani washegari kuma sai a rantsar dashi. Kafin nan, ranar 27 majalisar zartaswa zata yi taron karshe na bankwana da juna.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG