Shehu Sani yace dauko Tony Blair ya zo ya yi masu bayani akan gwamnati dake neman kawo canji bai dace ba.Yace kuskure ne jam'iyyarsu ta yi.
Shehu Sani yace zai kauracewa taron domin Tony Blair yana cikin shugabannin duniya da suka haddasa rikicin gabas ta tsakiya.Rigingimun da suka faru a Iraqi da Libya da sauran kasashen yankin duk da hannun Mr. Blair a ciki. Jam'iyya mai neman kawo canji babu abun da zata koya a wurin Tony Blair.
Malam Shehu Sani yace da za'a nemi shawararsa akwai mutane biyar da suka cancanta a gayyata. Akwai tsohon shugaban kasar Ghana. Akwai tsohon shugaban majalisar dinkin duniya. Akwai wasu shugabannin duniya daban daban da suka yi rawar gani kama daga Indiya zuwa China da kasar Brazil da suka kawo canji. Ana iya gayyatosu amma ba Tony Blair ba.
Tony Blair na cikin manyan shugabannin duniya guda biyu da suka haddasa yakin Iraqi da Libya kuma har yanzu kasashen basu kubuta daga yaki ba ko tashin hankali ba. Tunda aka hambarar da gwamnatin Sadam Hussen ba'a zauna lafiya ba. Saboda haka menene za'a koya daga mutane irin su Tony Blair. Shin zai koyawa 'yan Najeriya yadda zasu mamaye kasashen dake makwaftaka da su ne ko kuma yadda zata dinga yin yake-yake.
Ga rahoton Maina Kaina.