Taiwan Za Ta Tabbatar Da Wanzar Da Halayyar Walwala Da Dimokradiyya.

Taiwan Morris Chang

Shugabar kasar Taiwan Tsai Ing-wen ta ce duk wani “matsin lamba daga waje,” ba zai hana tsibirin mai cin gashin kan sa mu’amala da sauran duniya ba.  

A yau Laraba ne Tsai ta yi wannan furucin jim kadan kafin ta tashi a filin jirgin saman kasa-da-kasa na Taoyuan da ke Taipei, domin kai ziyarar aiki a Guatemala da Belize.

Ta fadawa manema labarai cewa Taiwan tana cikin kwanciyar hankali da kwarin gwiwa, yayin da kuma ba zata iya jurewaba amma kuma ba ta takalar fada.

Ziyarar ta Tsai ta tsawon kwana 10 a makwabtan kasashen tsakiyar Amurka, za ta hada da biyawa a birnin New York kan hanyarta ta zuwa Guatemala, da kuma Los Angeles bayan ta dawo kafin ta isa gisa.