Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama ‘Yan Gwagwarmayar Rajin Dimokradiyya Sama da 50 a Hong Kong


Sama da ‘yan gwagwarmaya 50 aka kama a birnin Hong Kong saboda sun saba wata sabuwar dokar tsaro ta birnin.

Sama da ‘yan gwagwarmayar rajin dimokradiyya 50 aka kama a birnin Hong Kong ranar Laraba 6 ga watan Janairu saboda sun karya wata dokar tsaro ta birnin mai cike da takaddama, a cewar kafafen yada labaran yankin, a wani farmaki mafi girma da aka gani a akan ‘yan jam’iyyar adawa ta Democratic a karkashin sabuwar dokar.

Kamen da aka yi a birnin da ake hada-hadar kasuwanci a nahiyar Asiya, ya hada da wasu sanannun ‘yan jam’iyyar Democratic da tsofaffin ‘yan majalisa wato James To, da La Cheuk Ting, da kuma Lester Shum, a cewar shafin yanar gizon jam’iyyar Democratic da kuma gidan rediyo da talabijin din Hong Kong na RTHK.

Nan take dai ‘yan sanda basu maida martini ba.

Shafin Facebook din jam’iyyar Democratic ya ce ‘yan sanda sun kama ‘yan gwagwarmayar ne saboda sun yi wani zabe mai zaman kansa da aka shirya a shekarar da ta gabata don zaben ‘yan takarar da zasu tsaya musu a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar da ke tafe, abinda gwamnatin Hong Kong da Beijing su ka yi gargadin cewa ta yiwu ya saba wa sabuwar dokar a lokacin.

XS
SM
MD
LG