Wata girgizar kasa da ta afkawa garin Tainan da ke kudancin Taiwan a yau Asabar ta halaka mutane 11, bayan da ta ruguza wani babban bene. Daga cikin wadanda suka mutu har da wani jariri.
WASHINGTON D.C. —
Rahotanni sun ce daruruwan mutane sun samu raunuka, yayin da hukumomin ke hasashen akwai mutane da dama da ginin ya rubta akansu.
Wata Cibiyar binciken Amurka, ta ce girgizar kasar mai karfin maki 6.4, ta faru ne kusan kilomita 40 a kudu maso gabashin garin na Tainan, wanda ke da yawan mutane kusan miliyan biyu.
Da misalin karfe hudu na safe agogon yankin girgizar kasar ta fara kada gidaje.
Hukumar da ke kula da yanayin kasar ta Taiwan, ta ce an ji hucin ta a wurare da dama.
A shekarar 1999 an taba samun wata mummunar girgizan kasa a kasar ta Taiwan.