Waɗannan allurai, haɗe da alƙawurra waɗanda aka yi tun daga watan Fabrairun 2021, za su ba da gudummawa fiye da allurai biliyan 1 a shekara mai zuwa. Amurka za ta ba da gudummawar rabin allurai.
"Babban abin da muka sa a gaba shi ne hanzarta fito da ingantattun alluran rigakafi, masu sauki da kuma araha ga kasashe masu fama da talauci, lura da muhimmancin yin allurar riga-kafi a matsayin amfanin jama'a na duniya," shugabannin G7 suka rubuta a wata sanarwa.
Shugaba Biden ya yi maraba da sadaukarwar yin tarihi wanda ya biyo bayan nasa sanarwar har zuwa taron - cewa Amurka za ta sayi allurai rabin biliyan na maganin Pfizer/BioNTech na COVID-19 don ba da gudummawa ga kusan kasashe 100 da tattalin arziki, gami da 92 marasa karfin tattalin arzikin, da masu matsakaicin karfi wadanda suke cikin tsananin bukatar yaki da wannan annoba. Kamar yadda Shugaban ya nuna, Amurka za ta sayi “mafi yawa na gudummawar rigakafin COVID-19 da kowace kasa ta taba yi.”
Shugaba Biden ya ce "Wadannan allurar rigakafin rabin biliyan za a fara jigilar su a cikin watan Agusta da sauri da ga fitowar su daga kamfani ." "Za a kawo miliyan dari biyu daga cikin wadannan allurai a wannan shekarar, a 2021, kuma za a isar da karin miliyan 300 a farkon rabin shekarar 2022."
Amincewar Amurka na ba da gudummawar allurar rigakafin Pfizer ta COVID-19 da ta kai rabin biliyan don yakin duniya ya zo ne a kan akalla allurai miliyan 80 da Shugaba Biden ya sanar a baya da dala biliyan 2 na kudin da Amurka ta bayar don tallafawa COVAX, hanyar ƙasa da ƙasa don sadar da allurar rigakafin COVID-19 mai lafiya da inganci.
Sabon alƙawarin da ƙasashen G7 suka sanar yana nufin cewa tun a shekarar 2020, abokan G7 ɗin sun himmatu wajen bayar da kuɗaɗe da samar da allurar rigakafin sama da biliyan biyu ga duniya. Kasashen G7 sun kuma himmatu wajen faɗaɗa samarwar cikin gida don aƙalla allurai na biliyan 1 na aminci da inganci na alurar rigakafin COVID-19 a cikin 2021 da 2022, gami da haɗin gwiwa kamar Quad Vaccine Partnership na Amurka, Australia, India, da Japan
Shugaba Biden ya lura cewa, akwai kyakkyawar fahimta a tsakanin kasashen G7 cewa alkawurran da suka yi kwanan nan ba suna nuna karshen kokarinsu na kawar da COVID-19 ba ne. "Wannan," in ji shi, zai zama aiki ne na wani tsawon lokaci. "