Kasar Amurka da kawayenta na G7, sun kasance cikin damuwa, game da yin amfani da kowane irin nau'in bauta wajen gudanar da ayyukan a sassan duniya ciki har da wanda kasashe suke marawa baya, kamar yadda ake ma ‘yan kabilar Uyghurs da sauran kungiyoyin kabilu da addinai, a Xinjiang, na Kasar Sin.
Bangarorin aikin gona, samar da wutar lantarki ta hanyar makamshin rana, da ma’aikatun da ake saka tufafi a Xinjiang su ne tushen samar da irin wadannan ayyuka.
Shugabannin sun amince kan mahimmancin tabbatar da 'yancin ɗan adam kuma sun himmatu don kare mutane daga aikin bauta.
Bugu da kari, kasashen G7 sun kuduri aniyar hada karfi da karfe wajen magance barazanar yin kutse ta yanar gizo kan na’urorin zamani. An sami gagarumar kutse ta yanar gizo da ke shafar yawancin membobin G7 da sauran manyan ƙasashe, mahimman masana'antu, da kamfanonin lantarki, da asibitoci.
Kungiyoyi masu aikata miyagun laifuka na kasa da kasa, kan far wa muhimman ababen more rayuwa, fannin sarrafa kudade ta yanar gizo, da halalta kudaden haram, tare da kaikaitar mutane da dama a duniya. Ya zama dole bangaren gwamnati da na masu zaman kansu, su hada kai don ganin cewa an kare ababen more rayuwa.
Bugu da ƙari, dole ne a binciki ayyuka na ɓoye a kuma hukunta masu aikatawa tare da samar da makari mai inganci. Akwai bukatar kasashe a mataki na cikin gida, su yi kokari su magance wadannan matsaloli da ke faruwa a cikin kasashensu.
Kasashen G7 sun kuma amince su dauki matakin gama gari don yaki da cin hanci da rashawa. Kwanan nan Shugaba Biden ya ayyana kokarin dakile cin hanci da rashawa a Amurka ya kuma ba da Takardar Nazarin Tsaro ta Kasa kan Yaki da Cin Hanci don daukaka wannan muhimmin aiki.
Rashawa na kashe jama’a kwarin gwiwa; yana kassara ayyukan gwamnati , tare da barnatar da dukiyar jama'a; kuma yana cinye turakun da aka ginin al'ummomin dimokiraɗiyya. Bugu da kari, cin hanci da rashawa na haifar da asara mai yawa ga tattalin arziki kuma rashin adalci ne ga 'yan ƙasa.
Tare da kawayenta na G7, Amurka za ta magance rashin amfani da kamfanonin kwata-kwata, iyakance karfin mugayen ‘yan wasa don barnatar da kudin datti a saye da sayar da gidaje, inganta musayar bayanan da suka shafi cin hanci da rashawa, da sake fasalin taimakon kasashen waje don mai da hankali kan cin hanci da rashawa a matsayin gigiya-kankan fifiko.
Kasar Amurka na maraba da wannan yunkuri na G7 game da hada kai don magance cin hanci da rashawa.
Kamar yadda Shugaba Biden ya ce, "Amurka ta dawo jagorancin duniya tare da sauran kasashe da ke da muradu irin nata.