Wata-taho-mu gamar da ta kusa aukuwa tsakanin jiragen ruwan China da Amurka akan tekun kudancin China da ake takaddama akai, ta girgiza kasashen Asiya.
Jirgin Amurkan ya kusanci na China da kimanin mitoci 40 a tekun kudancin china, a ranar 30 ga watan Satumba, wanda ya yi sanadiyar jirgin Amurka ya canza hanya shi, a cewar ma’aikatar Pentagon.
China na ikirarin cewar kashi 90 na tekun ita ke iko da shi, amma Amurka ta ce sauran kasashe ma na da hakki akai.
A ranar Asabar shugaban tsaro daga tawagar mutane 10 na kungiyar jiragen ruwa na kudancin Asiya, ba su amince da wannan matakin ba, hakan ya sa suka bukaci a yi wani taro a Singapore don bayyanar da hakkin kowa, da kuma sanin hurumin China daga Amurka.
Kasashen dai sun nuna damuwarsu, don hatsarin ka iya faruwa nan gaba, da kuma tsoron haramta amfani da tekun da Amurka ke kokarin yi.