Tabarbarewar Tsaro Da Ilimi a Arewacin Najeriya

Wasu daga cikin wuraren da aka kai hare-hare

Wasu daga cikin wuraren da aka kai hare-hare

Shugabannin hukumomi dake bada ilimi na jihohi talatin da shida na Najeriya sun yi taron inda suka tabo yadda tabarbarewar tsaro ta shafi ilimi
Yadda har mutane rike da bindigogi zasu shiga makarantu su kashe yara da malamai a jihohi kamar su Yobe da Borno abun damuwa ne. Lamari ne da gwamnoni da shugaban kasa ya kamata su tashi tsaye domin yana yiwa ilimi rauni a arewa da ma kasar.

Da a Najeriya ana daukan yara daga Legas zuwa Maiduguri ko Sokoto ko kuma daga Gusau zuwa Oyo ko daga Kano zuwa Ibadan ko dai wani gari daban. To yanzu a halin da ake ciki iyaye na shakkan barin 'ya'yansu su yi nisa da su ba domin komi ba domin rashin tsaro har ma a makarantu.

Taron shugabannin ilimin ya tabo batun samarda malamai nagatartu a makarantun framare da sakandare ba na bogi ba. Kamata yayi kafin a dauki malamai a bincikesu. A tabatar suna da takardun shaida na ilimin da suke ikirarin sun samu kana a bi digdigi. Sun yi misali da jihar Pilato inda malamai fiye da dubu daya suka ce sun yi karatu a makarantar horar da malamai a Gindiri. Da aka bincika mutane takwas ne kawai suka yi karatu a makarantar. Duk sauran na bogi ne. Domin haka dole a binciki malamai kafin a daukesu aikin koyas da yara.

Mustafa Nasiru Batsari nada karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Tabarbarewar Tsaro Da Ilimi a Arewacin Najeriya - 2:45