Takardamar dake tsakanin bangarorin biyu sai dada tsamari yake yi. Babu wanda yake sauraran wani. Yayin da ake zantawa da mutanen jihar da ma 'yan cirani mutum na farko ya ce shi baya son gwamna Amechi domin bai yi wani aikin a zo a gani ba a jihar. Babu abun da ya sa gaba illa barnar kudi da ya ce bashi da wani anfani.Wani dan jihar kuma ya ce shi yana gani gwamnan ya yi kokari matuka musamman ta bangaren ilimi da kuma ayyukan raya kasa yayin da shekaru da dama ba'a ga irin ayyukan ba. Ma'ana babu wani gwamnan jihar da ya yi aikin da Amechi ya yi.
Shugaban kungiyar kawayen mutanen Rivers ya ce a gaskiya gwamna Amechi yana aiki. Ya ce idan aka duba baya babu wani gwamna da ya yi aikinsa. Ya bada misali da hanyoyi da gwamnan ya yi. Ya ce wuraren da ba'a zato za'a samu hanyoyi ba sai yau gashi an samu hanyoyi.Wani ya ce zaman lafiya da aka samu lokacin Amechi ba za'a iya kwatantashi ba.Wani ya ce wanda ya yi shekara goma bai zo Fatakwal ba yau in ya zo zai bata domin cigaban da aka samu karkashin Amechi.
Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto.