A yanzu hakka ana shirin sakin masu garkuwa da mutanen da aka kama, wanda kuma ake ganin zai iya kawo barazana ga al'ummar masarautan Shani.
Mai martaba ya baiyana hakan ne lokacin da Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ziyarci masarautar Shani, dan ganewa idanunsa irin yadda al'amura ke gudana da kuma daukan alkawari na sake inganta matakan tsaro.
Alhaji Mailafiya, ya ce su a garin Shani suna zaman lafiya da al'ummar su, sai dai wannan sabuwar matsala ta sace-sacen jama'a da karbar kudin fansa ta zamar musu ruwan dare, haka kuma tun da aka kama mutanen da ake zargin cewa su suke aikata wadannan laifuffukan, abin yayi sauki sai dai yanzu kuma suna jin cewa za a saki wadannan mutanen. Hakan kuwa zai iya jefa mutanen Shani cikin hatsari.
Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda Biu.
Your browser doesn’t support HTML5
.