Masu Neman Kambin Zakaran Kwallon Kafa Na Duniya

Mujallar nan ta kasar Faransa mai suna Football Magazine France, wace take fidda sunayen ‘yan wasan da zasu kara wajan samun zama zakaran kwallon kafa na duniya na shekara 2017, ta bayyana sunayen ‘yan wasan kwallon kafa bangaren maza su 30.

Wadanda aka zaba zasu yi gogayya ne wajan fidda dan wasa daya tilo da zai lashe kambin zakarar kwallon kafa na duniya watau (Ballon D' Or) na shekarar 2017.

Wanda suka fito daga kasashe da nahiyoyi da kungiyoyin kwallon kafa daban daban a duniya.

A cikin ‘yan wasan akwai dan wasan gaba na PSG Neymar Jr, Luka Modric, (Real Madrid) Marcelo, ( Real Madrid) N'Golo Kante, (Chelsea) Paulo Dybala, (Juventus) Luis Suarez, (Barcelona) Sergio Ramos, (Real Madrid) Jan Oblak (Atletico Madrid) Philippe Coutinho, (Liverpool) akwai Dries Mertens, na (Napoli) da Kevin De Bruyne (Manchester City) Robert Lewandowski ( Bayern Munich).

Sauran sun hada da mai tsaron raga na Manchester United, David De Gea, sai Harry Kane, ( Tottenham) Edin Dzeko, (AS Roma) Antoine Greizmann (Atletico Madrid) Toni Kroos (Real Madrid) Gianluigi Buffon, ( Juventus) Sadio Mane, (Liverpool) Radamel Falcao, ( AS Monaco)

Lionel Messi daga (Barcelona) Pierre-Emerick Aubameyang (Borussia Dortmund) Edinson Cavani (PSG) Mats Hummels Bayern Munich) Karim Benzem, (Real Madrid) Cristiano Ronaldo, (Real Madrid) Eden Hazard, (Chelsea) Leonardo Bonucci, (AC Milan) Isco Alarcon, daga Real Madrid daga karshe akwai matashin dan wasannan mai shekaru 18, dan kasar Faransa Kylian MBappe na PSG.

Your browser doesn’t support HTML5

Sunayen Masu Fafatawa Cin Kambin Dan Kwallon Kafa Na Duniya - 4'08"