Wasu yan sahun gaba, masu ra'ayin rikau na cikin jamiyyar Republican, a majilisar wakilan Amurka sun yi alkawari haifar da rudani wajen zaben wani sabon kakakin majilisar da za ayi yau din nan.
Masu wannan ra'ayin dai a jiya laraba sun ce suna mara wa wakilin da ya fito ne daga mazabar Florida baya, wato Daniel Webster, inda suka yi fatali da kokarin da sauran yan majilisasr keyi na ganin cewa wakili daga Califonia Kevin McCarthy ya dare kan shugabancin majilisar,domin ko shine mataimakin Boehner da yayi murabus, kumayana da goyon yan majilisar har su 247.
To sai dai kuma idan har dukkan su su 40 dake wannan ikirarin suka jefa wa Webster kuria wannan zai hana McCarthy damar maye gurbin na Boehner a matsayin kakakin majilisar.
A cikin watan da ya gabata ne dai Boehner ya bayyana cewa zaiyi murabus daga shugabancin majilisar wakilan na Amurka, bayan ya kwashe shekaru 25 a majilisar, kana yayi shekaru 5 a matsayin kakakin majilisar.