Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Nemi Gafara Game da Hari Akan Wani Asibiti dake Kunduz


Shugaba Barack Obama na Amurka yayinda ya kira shugabar kungiyar likitocin da ake kira Doctors Without Boarders
Shugaba Barack Obama na Amurka yayinda ya kira shugabar kungiyar likitocin da ake kira Doctors Without Boarders

Harin da sojojin Amurka suka kai kan wani asibiti a Kunduz dake kasar Afghanistan bisa kuskure ya nemi gafara daga shugabar kungiyar likitoci masu bada agaji

Shugaban Amurka Barack Obama ya nemi afuwar kungiyar aikin agajin nan ta Doctors without Borders game da harin bam din Amurka har ya fada kan asibiti a Kunduz da ke Afhghanistan.

Sannan harin ya hallaka mutane 22 a karshen makon da ya gabata. Kakakin fadar White House Josh Ernest yace, Mista Obama ya bugawa shugabar kungiyar taimakon ta Likitoci Joanne Liu ya bada hakuri da yin ta’aziyya.

Obama ya yi kira ga Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani da ya bayyana ta’aziyyarsa game da rasa rayukan wadanda basu ji ba ba su gani ba da aka yi wannan harin ta sama. Kamar yadda Josh ya bayyana.

Kungiyar ta Doctors without Borders da akan kira MSF da Faransanci a takaice, ta bukaci a yi bincike bisa ka’idar yarjejeniyar kasa da kasa game da yaki ta Geneva.

XS
SM
MD
LG