Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alhazan Da Turmutsitsin Mina Ya Rutsa Dasu Sun Sauka a Nijar


Kimani Alhazai 300 ne na ayarin farkon Alhazan Nijar,wani jirgen kasar Saudi Arabia, ya sauke a filin jirgin sama Niamey

Kimani Alhazai 300, ne na ayarin farkon Alhazan Nijar,wani jirgen kasar Saudi Arabia, ya sauka dasu a filin jirgin sama Niamey, a daren jiya galibin Alhazan sun sauka da alamar gajiya a jikinsu yayin da waasu a fili ake ganin raunin da suka ji.

Wasu kuwa saida jami’an agaji suka taimaka wajen sauko dasu daga cikin jirgin saman sannan aka dora su akan keken guragu zuwa wani daki da aka kebe domin su.

Shugaban kasar Nijar Issoufou Mahamadou, yayi tattaki zuwa filin jirgin saman domin yiwa Alhazan Baraka da zuwa, ya kuma ce “mutane da yawa sun rasa rayukan su wasu kumasun tsira da rayukansu wasu kuwa dimuwa ta kamasu suka ba ce a kasa mai tsarki shi yasa na zo na yi masu ta’aziya na ‘yan uwa da suka rigamu gidan gaskiya.”

Tuni dai Gwamnati tayi tanadin wuraren na masamman a asiobitocin kasar ta Nijar, domin kula da lafiyar wadanda turmutsitsin na Mina ya jirkata, in ji Manu Agali, Ministan kiwon lafiya.

Ana sa rai fara jikilar sauran Alhazan, na Nija, zuwa gida daga ranar 12, ga wannan watan na Oktoba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG