Sun kai Hari Garin Minga da Mahaifar Hafsan Sojojin Najeriya

Wasu ‘yan Bindiga da ake zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun afkawa garin Minga, dake karamar hukumar Biu, a cikin jihar Borno, da hari inda suka kashe mutane takwas, wasu kuma suka samu raunuka.

Wannan harin na ci gaba da gudana bayan harin da aka kai garin Buratai, mahaifar Hafsan Sojojin Najeriya,Manjon janar Tukur Yusuf Buratai,inda suka hallaka wasu mutane biyu.

Wani da wakilin muryar Amurka Haruna Dauda, yayi hira dashi yace goshin Magariba aka soma ganin su a cikin garin Minga, bayan sallar Isha'i kuma sai aka gansun su kusab ashirin.

Hare haren na ci gaba da wakana ne ganin yadda hukumomin Soja keyi da gaske wajen farauto ‘yan kungiyar ta Boko Haram, da kuma fafutukar da suke yin a kawo karshen wannan hare hare masamman wannan sabon salon a kunar bakin wake.