Sun Karbo Kudi Bashi Sun Rabawa Juna

Mua'azu Babangida Aliyu

Gwamnatin jihar Neja, dake tarayyar Najeriya, tace zata bincike tsohowar Gwamnatin Dr. Mua’azu Babangida Aliyu, game da wasu makudan kudade da tace bata gane inda aka nufa dasu ba.

Sakataren yadda labarai na Gwamnan jihar Neja, Dr. Ibrahim Doba, yace a lokacin da aka kafa kwamitin karban mulkin jihar, an nuna masu cewar Gwamnatin Babangida Aliyu, ta bar bashin Naira Miliya dubu Hamsin da bakwai, amma a yanzu sun gano cewa akwai wasu abubuwa daban.

Dr. Ibrahim Doba yace “ Gwamnatin da ta shude sun dauki kudi bashi sun rabawa juna, domin sun dauki bashi za suyi aiki dashi basu yi aikin ba kudin nan kuma na mutane ne yanzu abun da muke so mu gayamasu shine muna son kudin mu a dawo mana da kudin mu kudin mutane ne ba nasu bane.”

Tsohon sakataren Gwamnatinjihar Nejan, Alhaji Idris Ndako, yace basu da wani shakku akan duk wani bincike da za;a yio masu.

Shima kakakin tsoho Gwamna Babangida Aliyu, Mr Israel Ebije, yace suna shirye da duk wani bincike daga sabuwar GHwamnatin jihar Nejan, ya kara da cewa idan zasu kafa kwamitin bincike suna iya kafawa mu dai bamu da wani shakku.

Gwamna Abubakar Sani Bello, yayi wani ganawa ta siri da Sarakunan gargajiya, wanda ake harsashen cewa batun kudaden da tsaro na cikin abubuwan da ganawa ta kunsa.