Gwamnan jihar Katsina Alhaji Bello Aminu Masari, ya ce yin sulhu da ‘yan ta’adda ba ya tasiri saboda ya gwada a jiharsa kuma ba a samu nasara ba kasancewar ‘yan bindigar ba a kungiya daya suke ba.
Wasu daga cikin jihohin arewacin Najeriya na fuskantar yawan tashin hankalin ‘yan bindiga a daidai lokacin da garkuwa da mutane don neman kudin fansa ke kara yawaita.
Missali na baya-bayan nan shi ne tsakanin ‘yan bindigar da suka sace daliban jami’a da gwamnatin jihar Kaduna, wadda ta hau kujerar naki wajen yin zama da ‘yan bindigar.
Garkuwa da mutane don kudin fansa lamari ne da ke neman zama ruwan dare a arewacin Najeriya,.
Sai dai wasu iyalai da gwamnatoci kan biya makudan kudade ga ‘yan bindigar don ceto rayukan wadanda aka kama, lamarin da wasu masana harkokin tsaro ke kallo tamkar karawa ‘yan bindigar kwarin gwiwa ne da karfi.
Jihar Katsina na daga cikin jihohin da suka sha fama da tashin hankalin ‘yan bindiga a arewacin Najeriya, kuma ta sha yunkurin yin sulhu da ‘yan bindigar amma kwalliya ba ta biya kudin sabulu.
Saurari tattaunawar gwamna Aminu Bello Masari da Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5