Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu Abubakar, ya jaddada shirin jami’an tsaro na kare jama’a tare da gargadin cewa duk wani dake shirin kawo rudani a zaben shugaban kasa ya sake tunani.
Shugaban ya ce satar akwatin zabe da zageranci da kuma saye ko sayar da kuri’a da bangar siyasa na zama manyan laifuka a lokutan zabe, haka kuma ya ‘kara da gargadin cewa duk wani da aka kama da daya daga cikin laifukan zai yabawa aya zakinta.
Mallam Kabiru Adamu, dake zama masanin tsaro a Najeriya, ya yiwa jami’an ‘yan sanda kyakkyawan fata ganin yadda shugaban hukumar zabe ya jaddada muhimmancin aikin ‘yan sanda a tsarin da ake da shi na bangaren tsaro a wuraren zabe.
Shi kuma Mallam Aliyu Shamaki, cewa ya yi shirin da ‘yan sandan su ka yi na tun karar zabe abu ne mai karfafa gwiwa.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.