Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Bindinga Sun Kashe Mutane 8 Akan Iyakar Nasarawa Da Binuwai


Wassu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari a kauyen Ebete dake yankin Agatu a jahar Binuwai, suka hallaka mutane takwas wassu hudu kuma suna kwance a asibiti ana musu jinya.

Kauyen na Ebete dai na gabar kogin Binuwai ne dake kan iyakar jihar da ta Nasarawa.

Wani mai suna Collins Edache, wanda dan uwa ne ga iyalin da aka kashe, ya ce lamarin ya auku ne da missalin karfe sha biyu saura kwata na daren jiya laraba.

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Binuwai, DSP Sewuese Anene ta shaida cewa lallai lamarin ya auku, sai dai a cewarta kwamishinan 'yan sandan jihar ne zai iya yin karin bayani.

Rahotanni dai sun nuna cewa mutane goma sha shida ne suka rasa ransu a harin na jiya laraba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:03 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG