Shugaban kasar Sudan ta Kudu, Salva Kiir, ya ce watannin da aka kwashe ana mummunan rikicin kabilanci na yin babbar barazana ga zaman lafiyar kasar.
Shugaba Kiir ya bayyana hakan ne yayin da kasar ke bikin cika shekara tara da samun ‘yancin kai a jiya Alhamis.
Yayin wani jawabi da ya yi wa al’umar kasar ta talbijin, Kiir ya yi kira ga daukacin ‘yan kasar da su hada kai domin tabbatar da zaman lafiya a kuma sasanta rashin jituwar da ke tsakanin al’umomin kasar, wacce “ta sha fama da yake-yake” a baya.
A cewar Kiir, yanzu kasar ta Sudan ta Kudu ta tsallake matakin fadace-fadacen siyasa, amma abin takaicin shi ne, yanzu tana fuskantar rikice-rikice a tsakanin al’umominta.
Ya kuma kara da cewa, “a matsayinmu na gwamnati, ba za mu bari a ruguza mana zaman lafiyar da muka samu ba.”
Shugaban Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Sudan ta Kudu, David Shearer, ya fadawa VOA cewa, daruruwan mutane sun mutu a watan da ya gabata a hare-haren daukar fansa da aka rika kaiwa a jihar da ake kira Jonglei.