Shugaba Muhammadu Buhari yace gwamnatinsa ba zata sake zama da kungiyar Boko Haram da sunan wata tattaunawa ba sai ta tantance ko waye ke jan ragamar kungiyar.
WASHINGTON, DC —
Shugaban na Nigeria yace har sau ukku yana bada umunrin a je a zauna a zanta da wadanan mutanen, amma yanzu yace ba zai kara dorawa akan hakan ba sai idan su jagabannin Boko Haram din sun fito fili, sun amsa cewa lalle sune ke jagorancinta.
A inda aka fiton nan dai an yi ta samu bayanai masu sabani inda Abubakar Shekau da tsohon kakakin kungiyar ta Boko Haram, kowanne ke fitowa yana cewa shine shugabanta.
Shugaba Buhari, wanda yace Boko Haram ta hallaka mutane sunfi dubu 20 tun daga lokacinda ta soma kaddamarda yaki kan ‘yan Nigeria a shekarar 2009, yace gwamnatin tashi ta kagara taga cewa ta kwato ‘yanmatan nan 200-da-wani abu ‘yan makarantar Chibok da mayakan Boko Haram suka sace a shekarar 2014.