Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Borno Na Kan Sake Gina Bama


 Gwamnan Borno Kashim Shettima
Gwamnan Borno Kashim Shettima

Gidaje da gine gine fiye da dubu goma ne 'yan kungiyar Boko Haram suka rushe ko suka konesu a garin Bama banda makarantun firamare goma da suka kone tare da asibitoci da wuraren more rayuwar jama'a

Kwamishanan ma'aikatar sake gina jihar Borno Dr Baba Gana ya shaidawa Muryar Amurka ayyukan shirin sake gina Bama da gwamnatin jihar ta sa gaba tunda gwamnan jihar ma ya tare a garin.

Yanzu dai ana kan sake gina gidajen mutanen da suka rasa muhallansu.Kwamishanan yace duk barnar da aka yi a jihar babu wadda ta kai ta Bama. Yace gwamnan jihar ya fada masu so soma aiki a Bama domin farfado da garin. Kwana goma ke nan da suka fara aikin kuma ba zasu tsaya ba sai sun ga inda zasu kai nan da karshen shekara.

Sake gina garin na bukatar kudi soasai saboda haka gwamnatin jihar zata nemi taimako musamman daga gwamnatin tarayya.

A halin da ake ciki kwamitin da gwamnatin Tarayya ta kafa da Janar T. Y Danjuma ke jagoranta tayi alkawarin gina makarantu da asibitoci.

Ga rahoton Haruda Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG