Inda hukumar Tarawa da raba kudaden shiga ta Najeriyar ta nuna rashin amincewa ga kiran sayar da kamfanin iskar gas na Najeriya ga ‘yan kasuwa don amfani da kudin wajen raya tattalin arziki. Mukaddashin shugaban hukumar Shattima Umar Abba Gana, yace raya kamfanin ya ci gaba da aiki a matsayin mallakar gwamnatin Najeriya ya fi alheri.
Abba Gana, ya bayar da shawarar Najeriya ta nemo lamani don samun kudin aiki maimakon sayar da kadarori masu muhimmanci, inda yace jama’ar Najeriya na son tattalin arzikin kasar ya rinka bunkasa, amma idan ana sayar da su ta yaya zasu bunkasa.
Mukaddashin shugaban hukumar tara kudaden ya bukaci masu zuba jari da duk masu hannu da shuni su kafa sabbin kamfanoni maimakon neman sayan kamfanoni mallakar daukacin al’ummar Najeriya. Tuni dai ministan kasafin kudin Najeriya Udoma Udo Udoma, yace sayar da kamfanonin ba zai shafi mafiya muhimmanci ba.
Saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.