Sowore Ya Samu Gudummuwar Kudin Yakin Neman Takarar Shugabancin Najeriya

Omoyele Sowore dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress

Omoyele Sowore, mai fafutuka kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar African Action Congress AAC, wanda ke takarar neman zama shugaban kasar Najeriya a karo na biyu ya fara samun goyon bayan kudi daga masu hali baiwa.

A wata ‘yar gajeriyar sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, Mista Sowore ya yi kira ga masu hannu da shuni da su bayar da tasu gudummuwar wajen yakin neman zaben shugabansa kasa mai taken ‘yantar da Nijeriya baki daya, da cewa bai yarda da siyasar ubangida ba.

Tun bayan da ya yi wannan roko, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore ke karbar gudunmawa daga ‘yan Najeriya na gida da waje domin yakin neman zabensa na shugaban kasa a zaben 2023.

Masu ba da gudummawar sun yi hakan ne yayin wani taron tattara kuɗi na zahiri, mai taken, “Sowore Campaign Global Mega Fundraising,” wanda aka gudanar ranar Lahadi.

Wadanda suka bayar da tallafin sun hada da 'yan Najeriya da ke ciki da wajen kasar da suka bada gudummuwa a kudaden kasashen da su ke zaune.

Tara kudin yakin neman zabe ta k murka da kasashen Turai.

Mista Sowore ya ce idan aka zabe shi, gwamnatinsa za ta binciko amfani da kuma masana'antu sayar da tabar wiwi a matsayin wani bangare na kokarin inganta tattalin arziki da bunkasa fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje. Ya kuma yi alkawarin cewa, zai kawo sauye-sauye da za su amfani ‘yan kasa da kasar baki daya.

Idan ba a manta, a kwanakin baya bayan nan ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar African Action Congress, Sowore ya samu gudunmawa daga wata budurwa mai suna Loretta Oladayo, wadda ta baiwa dan takarar kyautar Naira miliyan daya don fara yakin neman zabe.