Omoyele Sowore, wanda ya kirkiro kafar yada labaran yanar gizo ta "Sahara Reporters" ya bayyana a gaban babbar kotun tarayya dake birnin Abuja a jiya Laraba, kuma an ba shi ranar da zai koma kotu don sauraren karar sa a watan Afrilu.
A can baya dai hukumar tsaron Najeriya ta SSS mai binciken sirri da yaki da ta’addanci, ta kama shi a watan Agusta.
An kama Sowore ne bayan da ya shirya wani gangamin neman juyin juya hali mai taken "Revolution Now", bisa hujjar rashin adalci a babban zaben kasa da aka gudanar bara. An sake shi a ranar 5 ga watan Disamba, aka kuma sake kama shi washe gari, kana aka sake shi a ranar 24 ga watan na Disamba, bisa umarnin ministan shari’a na kasar.
Matar Sowore ta fadawa muryar Amurka cewa ana azabtar da shi ne saboda fadar gaskiya da ra’ayinsa.
Facebook Forum