Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Zanga Zangar Neman Sake Omoyele Sowore


Masu Zanga zanga a kotu.
Masu Zanga zanga a kotu.

Magoya bayan tsohon dan takarar shugaban kasa a Najeriya da ake tsare da shi Omoyele Sowore, sun yi zanga zanga a wata kotu a Abuja inda ake sauraren shari’arsa.

An kama Sowore da wasu ‘yan fafutuka hudu ne a jajibirin shiga sabuwar shekara a wurin wani gangami juyin juya hali a Abuja na neman mulkin kwarai. Hukumomi sun tuhume shi da shirya taron da ya sabawa doka da kuma hadin baki wurin aikata laifi.

Sama da masu zanga zanga 70 dake cike da fushi a jiya Juma’a ne suka yita ihu a wata karamar kotun Abuja, suna kira a saki Omoyele Sowore nan da nan.

A farkon wannan mako, wani alkali da yake shari’ar ya hana bada belin da Sowore ya bukaci.

Sai dai ‘yan sanda basu zo da mutanen da ake tsare dasu a jiya Juma’a ba, kana kotu ta dage zaman ta.

Jagoran masu zanga zangar Kunle Ajayi da yaki yarda a kama shi a samamen da aka kai a ranar jajibirin sabuwar shekarar, ya ce za su ci gaba da zanga zangar. Ya kara da cewa idan ba a sake shi ba za su dauki mataki kuma hakan yasa suka je kotun domin yin zanga zanga.

Ajayi ya fada cewa an gudanar da zanga zangar ta ranar jajibirin sabuwar shekara cikin lumana har sai da ‘yan sanda suka isa wurin.

Masu fafutuka biyar ciki har da Sowore ne aka kama a ranar kana ake tsare dasu tun daga lokacin, ba tare da basu kulawa sosai ba wurin abinci da ruwa da kuma kiwon lafiya.

Hukumomi sun kira zanga zangar da taron da ya sabawa doka, a wannan mako kuma kafafen yada labarai cikin gida sun ce an zargi ‘yan rajin da hadin baki wurin aikata laifi da kuma yunkurin iza mutane su yi bore.

Karin bayani akan: Muhammadu Buhari,​ Omoyele Sowore, Nigeria, da Najeriya

XS
SM
MD
LG