Southampton Ta Koma Rukunin ‘Yan Dagaji

'Yan wasan Southampton

Shekarar Southampton 11 a gasar ta Premier League.

Southampton ta zama kungiya ta farko da ta koma rukunin ‘yan dagaji wato relegation a gasar Premier League ta Ingila.

Hakan na zuwa ne bayan da ta sha kaye a hannun Fulham da ci 2-0. Shekarar Southampton 11 a gasar ta Premier League.

Duk da ta fice daga gasar ta Premier, ya ragewa Southampton wasanni biyu.

‘Yan wasan Fulham Carlos Vinicius da Aleksandar Mitrovic ne suka ci wa kungiyar kwallayenta.

Firai ministan Birtaniya Rishi Sunak wanda masoyin kungiyar ta Southampton ne, ya halarci wasan da ya kai ga ficewar ta daga gasar.