Rahotanni daga Somaliya na cewa an kashe sojojin hadin gwiwa na kungiyar tarayyar kasashen Afrika ta AU da dama, bayan da mayakan Al- Shebab suka kai wani hari a wani sansanin sojin da ke garin Leego a kudanchin kasar a yau Juma'a.
WASHINGTON, DC —
Wadanda suka shaida lamarin sun ce, maharan sun gwabza wata mota shake da bama-bamai a jikin kyauren shiga sansanin, suka kuma fara musayar wuta da dakarun Burundi dake tsare da kofar.
Bayanai sun ce an kwashe sa'oi da dama ana bata-kashi bayan harin na farko.
Wani mai magana da yawun kungiyar ta Al Shebab, ya ce sun kashe fiye da sojojin hadin gwiwa sama da 50.
Gwamnan yankin Shabelle Abdikadir Mohammed Nur Siidi, ya tabbatar da cewa lallai an jikkata sojojin da dama.
A tadin da ya yi da Sashen Somaliya na Muryar Amurka, gwamnan ya kara da cewa suma mayakan al-Shebab an kashe su da dama, inda ya ce daga cikin su akwai 'yan kunar bakin-wake su 15 da suka tarwatsa kansu da bama-bamai.