Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SOMALIYA: John Kerry a Mogadishu Babban Birnin Somaliya


Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry da Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud a Mogadishu, Somaliya, May 5, 2015.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry da Shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud a Mogadishu, Somaliya, May 5, 2015.

A karon farko cikin shekaru ashirin John Kerry sakataren harkokin wajen Amurka ya zama babban jami'in Amurka da zai kai ziyara kasar Somaliya, kasar da ta dade tana fama da mugun ta'adancin masu tsatsauran ra'ayin Islama

Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry ya kai wata ziyarar da ta shiga tarihi a Somaliya jiya Talata, inda ya zama babban jami'in diflomasiyyar Amurka na farko, da ya kai ziyara a wannan kasa da yaki ya daidaita.

Wakilin Muryar Amurka dake cikin tawagar Kerry, Pam Dockins, ya ba da rahoton cewa Sakataren ya shafe kimanin sa'o'i uku da rabi a filin jirgin saman Mogadishu, inda ya gana da Shugaba Hassan Sheikh Mohamud, da Firayim Minista da kuma sauran jami'an kasar.

Ministan Harkokin Wajen Somaliya Abdisalam Hadliye Omer, ya gaya wa Sashin Somaliyanci na Muryar Amurka cewa, wannan ziyarar ta nuna cewa an samu cigaba a Somaliya, kuma lokaci ya yi na harkokin kasuwanci a kasar.

Ya ce tattaunwarsu da Kerry ta fi mai da hankali ne kan batun karfafa gwamnatin Somaliya da kuma yiwuwar sake bude ofishin jakadancin Amurka a babban birnin kasar.

Bayan tsawon shekaru 20 cikin rudu da tashin hankalin da ya ki ci ya ki cinyewa, babban birnin na Somaliya ya kara zama mara hadari cikin 'yan shekarun da su ka gabata -- to amma har yanzu gwamnatin na fama da hare-haren kunar bakin wake da kungiyar al-Shabab mai alaka da al-Qaida ke kaiwa.

XS
SM
MD
LG