A wasu sassa na jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya, jama'a na jaddada yin kira ga hukumomi akan a kai musu dauki saboda hare haren 'yan bindiga masu yin garkuwa da mutane.
Wannan la,ari dai ya sa wasu al'ummomi a arewacin Najeriya ci gaba da kasancewa cikin yanayin fargaba da tashin hankali saboda maharan duk da cewa mahukumta na kan kokarin shawo kan matsalolin.
Al'ummomin yankin jihar Sokoto da ke makwabtaka da jihar Zamfara, wadanda suka fuskanci hare haren ta'addanci lokacin da ake fafatawa da ‘yan bindiga a jihar ta Zamfara, sun sake samun kansu cikin mayucin hali sanadiyar waiwayowar matsalolin na hare haren 'yan bindiga.
Ko a karshen makon nan sai da mahara suka kai farmaki a wani gari mai suna Tafkin Kaiwa a karamar hukumar Dange-Shuni inda suka hallaka mutum daya suka kuma yi garkuwa da wasu.
Mai unguwar yankin ya ce suna cikin tashin hankali sanadiyar hare haren na ‘yan bindiga.
Shi kuma shugaban karamar hukumar ta Denge-Shuni, Umar Budah Gidan Gara, ya ce su na neman dauki domin matsalolin na ci gaba da daidaita yankunan su.
A nata bangaren rundunar 'yan sandan Najeriya, ta nemi goyon baya daga jama'a a kokarinta na kare rayuka, kamar yadda kakakinta a Sokoto ASP Sanusi Abubakar ya fada.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5