Cikin wannan mako an samu asarar rayukan mutane a kalla takwas, biyo bayan wata fafawata tsakanin yan bindiga da yan Banga a jihar Sokoto dake arwa maso yammacin Najeriya.
Yan bindigar sun fafata da yan Banga a garin Gatawa dake karamar hukumar Sabon Birni jihar Sokoto.
Daya daga cikin yan banga da suka fafata da barayin Saminu Hamidu, ya bayyana cewa matsalar ta fara ne lokacin da wasu Fulani ke kiwo, ganin ‘yan Banga kusa ya sa suka gayyato masu dauke da makamai daga Gangara, nan ne fa suka shiga musayar wuta da juna a karshe dai an rasa ‘yan Banga takwas.
A cewar Saminu, duk safiya sai ‘yan bindiga sun fito su tare hanya suna daukar mutane, ko kuma su kai hari a wasu wurare.
Yunkurin jin ta bakin kakakin rundunar yan sanda ASP Ahmad Rufa’i ya ci tura kafin hada wannan rahoto.
Wannan na zuwa ne lokacin da jama'a musamman mazauna yankunan da ke da matsalar rashin tsaro, ke cike da fata kan kalaman da sabon shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya yi akan tsaro su kasance hanyar kawo karshen matsalar.
Masana lamurran tsaro na ganin akwai manyan kalubalen tsaro masu yawa da za su iya zama tarnaki ga yunkurin sabon shugaban Najeriya kan alwashin samar da tsaro.
Har yanzu dai mazauna wasu yankunan na ci gaba da zaman dar-dar saboda rashin tsaro, duk da yake wasu na kyautata fatan yuwuwar samun mafita daga matsalolin.
Domin karin bayani saurari rahotan Muhammad Nasir.
Your browser doesn’t support HTML5