Daya daga cikin yunkurin na asusun UNICEF shi ne samar da wasu cibiyoyi na horas da almajirai da 'yan mata masu tasowa wadanda ba su samu damar zuwa makarantun boko ba, yadda zasu koyi ilimin na'urar komfuta da na yanar gizo.
Humukomomi sun jima suna nuna damuwa akan yawaitar yaran da basu samu damar shiga makaranta ba, musamman a arewacin Najeriya, tare da daukar matakai na kyautata rayuwar su.
Wani bincike da asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar tare da hadin guiwar hukumar kula da ilimin larabci da addinin Musulunci, da ma'aikatar mata ta jihar Sakkwato, sun tantance yara almajirai da 'yan mata masu tasowa da adadin su ya kai 249,523 wadanda ke bukatar dauki.
A kan hakan ne asusun na UNICEF tare da samun tallafin kudi daga gidauniyar Eleva dake kasar Burtaniya, ta samar da wasu cibiyoyi domin koya wa wadannan yara dabarun samun rayuwa kyakkyawa a nan gaba.
A hirar shi da Muryar Amurka, Micheal Juma jami’in gudanarwa na asusun UNICEF mai kula da jihohin Sakkwato, Kebbi da Zamfara yace an samar da katamfariyar cibiya don a koyawa yara da 'yan mata sana'o'i ta yadda zasu iya dogaro ga kansu, su kuma bada cikin al'umma nan gaba.
A nashi bayanin, Muhammad Maikudi jami'in kula da fasahar zamani na asusun unicef, yace za'a hada wa yaran komfutoci, a koya musu yadda ake amfani da yanar gizo, a kuma rika koya musu karatun alkur'ani ta amfani da yanar gizo, da sauran dubarun amfani da yanar gizo.
A nata bangaren, gwamnatin Sakkwato ta yi alkawarin kula da dorewar cibiyoyin da kuma rayuwar yaran da za su amfana da shirin.
Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5