Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Ilimi: UNICEF Ta Bukaci Gwamnatin Najeriya Ta Dauki Matakin Gaggawa Na kare Makarantu A Kasar


Wasu yara a wani shirin UNICEF
Wasu yara a wani shirin UNICEF

Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana bukatar kara kaimi wajen inganta batun kiyaye lafiya da tsaron makarantun najeriya.

Da ta ke bayani yayin bukin ranar ilimi ta bana, Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Ms. Cristian Munduate tace, a yayin da Najeriya ta nuna aniyar samarda kyakkyawan yanayi a makarantu ta hanyar aiwatar da yarjejeniyar kare makarantu tare da samarda ka’idojin tabbatar da hakan, har yanzu akwai sauran damar ingantawa.

“A wannan muhimmiyar rana, muna sane da hakkin daya rataya a wuyanmu na kare makarantu domin ‘ya’yanmu.” In ji ta.

Munduate ta kara da cewar, sau da dama neman ilmi na gamuwa da cikas sakamakon hare-haren da ake kaiwa al’ummomi da makarantu, al’amarin dake kaiwa ga satar dalibai.

Wadannan kalubale sun fi tasiri akan ‘yanmata, abinda ke kara kassara karatun ‘ya’ya mata a Najeriya.

UNICEF tace hare-haren baya-bayan nan akan makarantu, musamman a shiyoyin arewa maso gabas da yammacin Najeriya, sun kassara karatun fiye da yara milyan 1 da dubu 300, abinda ya sabbaba daukar matakan rigakafin rufe makarantun.

Hakan, in ji UNICEF, ya sake bayyana mahimmancin daukar matakan gaggawa na magance matsalar rashin tsaro a makarantu yadda ya dace.

Asusun na UNICEF ya kuma bukaci a dauki mabambantan matakan inganta tsaron makarantu, duba da kwazon da jihohi suka nuna wajen daukar matakan tabbatar da tsaro a makarantu.

Wannan mataki ya kamata ya kunshi samarda cikakken tsari da kulawa tare da samarda wadatattun kudade, musamman a jihohin dake fama da rashin tsaro.

Munduate ta bayyana aniyar UNICEF na ci gaba da aiki tare da gwamnatin Najeriya da masu bada gudunmawa da kungiyoyin bada agaji wajen tabbatar da cewar kowane yaro ya samu ingantaccen ilmi cikin zaman lafiya da tsaro.

Kididdigar baya-bayan nan ta nuna cewar, a bisa kiyasi, kaso 43 cikin 100 ne kacal na ka’idojin kiyaye makarantu aka cika a kimanin makarantu 6000 da aka nazarta, UNICEF ya tabbatar da samun wannan katafaren ci gaba na baiwa yara milyan 7 da 200, 000 damar samun ilmi a sansanonin ‘yan gudun hijra dake fadin Najeriya, sakamakon hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu tallafawa da kuma kungiyoyin bada agaji.

Wannan bincike ya haska irin kalubalen dake akwai wajen kiyaye gine-ginen makarantu tare da takaita hatsarin tashe-tashen hankula da bala’o’i.

Taken ranar ilmi ta bana, “ilmi domin samun dawwamammen zaman lafiya, ya tuna mana irin mahimmancin da ilmi keda shi wajen samun wanzuwar zaman lafiya da daidaito.

"Wannan matashiya ce ga dukkanin masu ruwa da tsaki-da suka hada da gwamnatocin tarayya dana jihohi, kungiyyoyin raya kasa dana fafutukar farar hula da al’umma da sauran masana game da muhimmancin samar da makarantu masu cikakken tsaro", in ji ta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG