SOKOTO: Hukumar NDLEA Ta Kama Masu Shaye-shayen Miyagun Kwayoyi Fiye Da 50

NDLEA ta kama dillalen miyagun kwayoyi

Hukumar yaki da sha ko tu'ammuli da miyagun kwayoyi a Najeriya ta hada hannu da sauran jami'an tsaro domin kara tsaftace al'umma daga illolin tu'ammuli da miyagun kwayoyi, yayin da shekara ta 2023 ke bankwana, bukukuwan Kirsimati da sabuwar shekara ke kara matsowa, .

A lokacin wani samame na hadin gwiwa hukumar ta damke mutane fiye da hamsin a Sakkwato, hadi da wani dilan kwaya wanda ya yi sanadin yi wa jami'in hukumar kisan gilla.

Tun ba yau ba ne 'yan Najeriya ke kokawa akan yadda illolin sha ko tu'ammuli da miyagun kwayoyi ke addabar jama'a, duk da yake mahukunta na cewa suna kokarin rage yawaitar matsalar.

Wasu ma na ganin cewa ko ayyukkan ta'addanci da suka dabaibaiye Najeriya suna kara habaka ne ta amfani da miyagun kwayoyi, kamar yadda wani dan gwagwarmaya, Abubakar Mailato ya fadi.

NDLEA ta kama dillalen miyagun kwayoyi

Bisa yawaitar koken jama'a tun ma ba yanzu ba da shekarar 2023 ke bankwana lokacin da ake fuskantar bukukuwa, ya sa jami'an hukumar yaki da sha ko tu'ammuli da miyagun kwayoyi ta nemi yin hadaka da jami'an tsaro don kara azama ga kawar dawannan mummunar dabi'a.

Kwamandan hukumar ta NDLEA a Sakkwato Iro Adamu Muhammad yace sun yi kawance da jami'an Soji, 'yan sanda da sibil difens suka yi dirar mikiya a wasu wuraren da ake tuhumar masu shaye-shaye ke sharholiya kuma sun kama matasa fiye da hamsin maza da mata.

Yace zasu yi bincike su fitar da dilallan kwaya daga cikin su, su kai su kotu, sauran kuwa za'a yi musu gargadi da bayar da shawara don su daina wannan muguwar dabi'a.

Kwamandan hukumar ya ce zasu gaudanar bincike a kan sa kuma za'a yi duk abinda ya dace kan sa.

Masu lura da lamurran yau da kullum na ganin akwai bukatar gwamnatin Najeriya ta kara baiwa hukumar NDLEA kwarin guiwa da kayan aiki ingantattu , yayin da su kuwa jami'an hukumar su kara azama wajen kawar da matsalar tu'ammuli da miyagun kwayoyi daga cikin al'umma.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

SOKOTO: Hukumar NDLEA Ta Kama Dillalen Miyagun Kwayoyi Fiye Da 50